El-Rufa’i Matsala Ne A Jam’iyyar APC – Jigon APC

An bayyana Gwamna El Rufa’i na Jihar Kaduna a matsayin wata matsala da Jam’iyyar APC ke fama da ita wanda ya dace a ɗauki matakan da suka dace wajen yi wa tufka hanci kafin ya jefa Jam’iyyar cikin tsaka mai wuya a daidai lokacin da babban zaɓe ke ƙaratowa.

Bayanin hakan na ƙunshe ne a cikin wata buɗaɗɗiyar wasiƙa da wani jigon Jam’iyyar kuma mai kishinta a Jihar Kaduna Auwal Nuhu ya aike wa Shugaban jam’iyyar na ƙasa Sanata Abdullahi Adamu domin ɗaukar matakin gaggawa.

Abin da tsohon shugaban ƙasa Obasanjo ya faɗi a kanshi ya tabbata a cikin littafinsa MY WACH inda ya bayyana shi a matsayin shu’umin mutum mara biyayya ga kowa sai a karan kanshi.

A fili ya ke Gwamna El Rufa’i ya jefa miliyoyin jama’a cikin ƙunci da takurawa, tun bayan aiwatar da rusau da ya yi akan muhallin jama’a da kasuwannin lamarin da ya durƙusar da wasu har abada.

Hakazalika El Rufa’i ya runtse ido ya yi ta korar ma’aikata babu lissafi lamarin da ya jefa rayuwar miliyoyin mutane a Jihar cikin azabar rayuwa.
Ɓangaren kuɗin makaranta ya yi ninkin ba ninkin na kudaden makaranta da ya gagari kundila ya jefa iyayen yara cikin ha’ula’i.

Da gangan El Rufa’i ya yi watsi da ‘yan gida a harkar samar da bayar da kwangila ya tsallaka kudancin ƙasa ya bada wannan dama. Sannan ya kalmashe Jam’iyya da ‘ya’yanta ya jefa aljihu ya mayar da ‘ya’yan APC a Jihar Kaduna Mabarata.

Idan aka dubi waɗanda ke jan ragamar gwamnatin jihar dukkanin su baƙi ne ba ‘yan Jihar Kaduna ba, waɗanda El-Rufai ya dauko su ne domin wata manufa ta cutar da jama’ar Jihar.

Mutane irin su Jimi Lawal wanda dukkanin harkokin jiha ke hannunsa bakon haure ne daga jihar Ogun, hakanan PPS Salisu Suleman ɗan Jihar Nasarawa ne, Muyiwa Adekeye daga jihar Legas, sannan babban mai bada shawara kar tattalin arzikin Jihar Martins Akumazi Inyamuri ne, babban mai bada shawara kan raya jihar Dr Ayo Adedokun daga Kudu maso yamma ya ke, sannan babbar mai bada shawara kan cigaban jiha Mary Olarerin daga Kudu da sauransu da dama wadanda suka cika gwamnatin sa.

Hukumar SUBEB ya damkata hannun mijin kanwarsa daga Kano, KSDPC na hannun ‘yar uwarsa Hadiza Yahaya Hamza, KADGIS ya ba ɗan Jihar Nasarawa, Hukumar Fansho na hannun wata budurwa daga jihar Neja, Hukumar zirga-zirga ta jihar na hannun Austin Ogar daga jihar Binuwai, da sauransu da dama.

Gwamnatin Jihar Kaduna ta samar da wani shiri wanda ta yi wa lakabi da sunan KASHIM IBRAHIM FELLOWSHIP wanda aka faro tun a shekarar 2016 inda ake dauko wasu jama’a daga wasu jihohi suna zuwa Jihar Kaduna na tsawon shekara guda ana biyansu albashi mai kauri da sauran abubuwan more rayuwa, sauran jama’ar Jihar Kaduna kuwa ko oho!

Ga waɗanda aka ɗauka a wannan shekarar sunaye da Jihohin da suka fito…

1- Abdulhakeem Abdulkareem-Kwara state
2.Sharon takim-Cross river state

 1. Khalid Haruna -kaduna state
 2. Womiye Ojo-Osun state
  5 Sani Mohammed-Borno state
  6 Khalil sadiq Abubakar- Kaduna
  7 Ramlah Ibrahim Nok- Kaduna state
  8 Sharon Itua-Edo state
  9 Bushira Tomitope Balogun- lagos
  10 Chuku Chukuemeka- Abia
  11 David Aluga -Taraba state
  12 Dadah olatejuh Yusuf- Oyo state
  13 Jemima Jenifer Justus- Kaduna state
  14 Eyitayo Oladejo- Osun state
  15 Sumayya Iliyasu- katsina state
  16 Isa Jonathan Ayiga-state kaduna
  17 Muhammad Aminu Kabara-kano state
  18 Jamila Idris -Kogi state
  19 Hauwa Jummai Matankari-Sokoto state
  20 Veronica Pamm Igube- Nasarawa
  21 Azaki Mary Sabo-FCT
 3. Suleman Abdulmajid- Kaduna state
  23 Modibbo Dutse- kaduna state
  24 Umar Hamza Gado- Kaduna state.

“Mai girma Shugaban jam’iya tabbas akwai kura-kurai da tsananin son zuciya kan yadda El Rufa’i ke tafiyar da gwamnati a jihar Kaduna, ya karya ‘yan kasuwa ya talauta Ma’aikata ya jingine ‘yan asalin jiha ya dauko baƙi ya maye gurbin su dasu ya zama wajibi a ɗauki mataki a kai”.

Jam’iyyar APC a Jihar Kaduna ta shiga rudani komai ya tarwatse mata kowa ya juya mata baya hatta sojojin baka duk sun yi shiru ruwa ya ci makaɗi.

Labarai Makamanta