El-CLASICCO: Madrid Ta Doke Barcelona 2-1

Kungiyar kwallon kafa ta riyal Madrid ta doke abokiyar hamayyarta Barcelona a gasan laliga mako na 30 da aka fafata fillin wasan real Madrid dake kasar spaniya.

Tun farko dai Madrid ta fara jefawa barcelona kwallo a raga ta kafan ‘dan wasan gabanta Karim Benzema, ya jefa kwallon ne a minti na 13 da fara wasan, minti na 28 Kuma dan wasan tsakiya Kroos ya jefa kwallo na biyu a bugun mai karamin tazara ( Free kick). Anje hutun rabin lokaci aka dawo Madrid na ci 2 ba ko daya.

Cikin Minti na 60 da wasan ne, ‘dan wasan Barcelona Oscar Mingueza ya rama wa kungiyar sa kwallo daya. Haka akai ta fafatawa tsakanin kungiyoyin inda saura minti 4 a tashi wasa aka ba Casemiro jar kati sakamakon ketar da yayi wa dan wasan barcelona. Haka aka tashi wasa Madrid tayi nasara kan barcelona da ci 2:1

Wannan sakamako yaba Madrid damar darewa teburin laliga a karon farko tun ana mako na 9 a gasar laligar inda tun daga wannan lokaci a farkon watan junairun shekarar nan kungiyar Atlhentico Madrid ke kan teburin laliga sai barcelona a matsayi na biyu inda Madrid ke mataki na uku.

Wannan nasara yaba Madrid zama kan teburin laliga kamin gobe ATM su buga wasan su na mako 30 da kungiyar kwallon riyal betis dake mataki na shida a gasar laliga da maki 46.

Wa kuke ganin zai iya lashe laliga a kakar bana?

Labarai Makamanta