Hukumar da ke yaki da cin hanci da rashawa ta Najeriya EFCC ta sake gurfanar da tsohon gwamnan jihar Kaduna Mukhtar Ramalan Yero a gaban babbar kotun tarayya da ke Kaduna kan wasu zarge-zargen da ke da alaka da halasta kudin haram.
Hukumar na zargin tsohon gwamnan tare da wasu mutum uku da karbar cin hancin kudi da suka kai naira miliyan 700 daga hannun tsohuwar ministar albarkatun man fetur Diezani Alison-Madueke domin yin magudin zaben shugaban kasa na shekarar 2015.
Sauran mutum ukun da ake tuhumarsu tare da tsohon gwamnan sun hada da tsohon Ministan Makamashi Nuhu Wya da tsohon Sakataren gwamnatin jihar Kaduna Hamza Ishaq da kuma tsohon shugaban jam’iyyar PDP na jihar Haruna Gaya.
An karanto musu zarge-zargen a gaba kotun inda duka suka musanta hannu a zargin da ake yi musu.
Kotun dai ta dage sauraron karar zuwa ranakun 16 da 18 ga watan Janairu.
You must log in to post a comment.