EFCC Ta Nesanta Kanta Da Samamen Da Aka Kai Gidan Alkalin Kotun Koli

Rahotanni daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Hukumar EFCC ta bayyana cewa danganta farmakin da wasu jami’an tsaro su ka kai gidan Mai Shari’a Mary Odili ta Kotun Ƙoli, da Hukumar ƙarya ce don kawai a kawo saɓani tsakanin ɓangaren Shari’a da EFCC.

Cikin wata sanarwa da Kakakin Yaɗa Labaran EFCC, Wilson Awujeran ya fitar ga manema labarai a ranar Juma’a da dare, ya ce jami’an EFCC ba su kai farmakin ƙoƙarin yin bincike gidan Mary Odili ba.

Ranar Juma’a da dare ne dai jami’an tsaro su ka kewaye gidan Mary Odili, amma jami’an tsaron gidan ta su ka ce ba za su shiga ba, sai da sammacin kotu.

Mary Odili dai ita ce matar tsohon gwamnan jihar Delta Peter Odili, wanda ya shafe shekaru da dama ya na kulli-kurciya da EFCC. Tun bayan saukarshi daga mukamin gwamna cikin 2007 ya ke garzayawa kotu ana ba shi kariyar hana EFCC su bincike shi ballantana a gurfanar da shi.

Wasu rahotanni sun nuna cewa Mary Odili ta shaida wa jami’an tsaron cewa ba za ta bari su shiga gidan ta ba, saboda ba gidan mijin ta Peter Odili ba ne, gidan ta ne

Labarai Makamanta