EFCC: Kotu Ta Damka Wa Gwamnatin Tarayya Tarin Kadarori A Kano

Labarin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewa Wata babbar kotun tarayya ta bayar da umarnin kwacewa tare da mallaka wa gwamnatin tarayya wasu kadarori 24 wadanda yawancinsu gidajen sayar da man fetur ne sabbi a jihohin Kano da Kaduna da Borno da Cros River na wani babban soja.

Hukuncin wanda alkalin Justice N.E. Maha ya yanke ya biyo bayan bukatar da hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin zagon ƙasa EFFCC ta shigar ne, wadda a watan Mayu na 2020 ta samu izinin kotu na karbe kadarorin a matsayin wucin-gadi.

Hukumar ta ce kasancewar ba wanda ya fito ya kalubalanci matakin kwacewar saboda haka ne alkalin kotun, Justice Maha a ranar Litinin 14 ga watan Fabrairu, 2022 ya bayar da umarnin mallaka wa gwamnatin tarayya kadarorin.

Kadarorin guda 24 wadanda suna warwatse ne a jihohin Kano da Kaduna da Borno da Cross River sun hada da filaye da manyan shagunankasuwanci da gidajen man fetur, kudinsu jumulla ya kai naira biliyan 10 da miliyan 935.

Labarai Makamanta