Ebonyi Bata Da Alaka Da Biafra – Gwamna Umahi

Gwamna David Umahi na Jihar Ebonyi da ke kudancin Najeriya ya bayyana cewa karmata ‘yan wagga fargaba idan ɗan ƙabilar Igbo ya zama shugaban ƙasa, yana mai cewa jiharsa “ba za ta taɓa shiga yunƙurin kafa ƙasar Biafra ba”.

Kazalika gwamnan ya roƙi hukumomin Najeriya da su murƙushe duk wanda ke son tayar da hankali a yankinsu na kudu maso gabas.

Umahi wanda ya bayyana aniyarsa ta tsayawa takarar shugabancin Najeriya a jam’iyyar APC mai mulki, ya faɗi hakan ne a Abakaliki babban birnin jihar ranar Alhamis yayin wata liyafa da aka haɗa masa.

Labarai Makamanta