Duniyar Wasan Kwaikwayo Ta Yi Babban Rashi Na Rasuwar Kasagi

Rahotanni da muke samu daga Jihar Katsina na bayyana cewar Fitaccen marubuci kuma ɗan wasan Hausa, Alhaji Umaru Ɗanjuma wanda aka fi sani da Kasagi ya rasu.

Marigayin ya rasu ne a gidansa dake birnin Katsina da asubahin ranar Juma’ar nan.

Marigayin ya yi fice a fannin rubutun Hausa da wasan kwaikwaiyo, kusan a iya cewa su ne na farko-farko a ƴan wasan Hausa.

Haka kuma, shi ya rubuta sanannen littafin wasan kwaikwayon Hausa na Kulɓa Na Ɓarna.

An haife shi a birnin Katsina tsohuwar Jihar Kaduna a shekarar 1950. Ya yi karatu a Najeriya da Ingila, inda ya ware a fannin fina-finai.Ya bar mata biyu da ‘ya’ya 13.

Labarai Makamanta