Duniyar Fina-Finai: Jarumi Kumurci Ya Angwance

Labarin da muke samu daga birnin Kano na bayyana cewa bayan kusan shekaru ashirin da rasuwar rabin ransa, jaruma Balaraba Muhammad, jarumi Shu’aibu Lawan wanda aka fi sani da Kumurci ya sake angwancewa.

Wani ma’abocin amfani da kafar sada zumunta ta Facebook mai suna Ahmed Prince Gandujiyya ya wallafa hotunan a shafinsa.

Gandujiyya ya shaida cewa Kumurci ya taba wani auren bayan jaruma Balaraba ta rasu amma Allah ya yi wa sabuwar amaryar rasuwa.

Kamar yadda gandujiyya ya sanar: “Ango Sha’aibu Lawan (Kumurci) ya yi sabon aure tun bayan shekaru 18 da rasuwar Matar sa Balaraba.

“Amma wasu rahotannin sun yi nuni da ya taba yin aure bayan rasuwar marigayiya Balaraba ya auri Maryam Umar ita ma ta rasu.

Labarai Makamanta