Duniyar Fina-Finai: Jaruma Maryam Jan Kunne Ta Dawo Fim


A yanzu haka dai tsohuwar jaruma a Masana’antar shirya Fina finan hausa Kanywood Maryam Jankunne ta dawo harkar fim bayan ta shafe tsahon shekaru da ba a ganin fuskarta a cikin Masana’antar.

Maryam ta shiga harkar fim a shekarar 2005 daga bisani tayi Aure a shekarar 2008. Jankunne na daya da ga cikin jarumai mata da suka taka rawa a masana’antar Kannywood a shekarun baya kafin tayi Aure.

Maryam tayi zamani da irin su Fati Muhammad, Rukayya Dawayya, Rashida mai sa’a, Mansurah Isah da sauran jaruman da suka yi fice a wancan lokacin.

Jarumar ta yi fina finai irinsu Jankunne kusan fim dinta na farko da ya fara fito da shi ne kuma ta samu lakabin Maryam Jankunne a cikin shirin.

A yanzu haka ana tsaka da daukar sabon wani shirin da Maryam fito a cikinsa mai Suna AKASI shirin mai dogon zango, ya dauki jarumai kamar haka Abba El Mustapha, Saratu Gidado wato Daso da sauran jarumai.

Labarai Makamanta