Duniyar Fina-Finai: Jaruma Halima Atete Za Ta Amarce

Labarin dake shigo mana daga jihar Kano na bayyana cewar fitacciyar Jarumar Kannywood Hajiya Halima Atete za ta amarce a Kwanan nan.

Tauraruwar Kannywood Halima Yusuf Atete za ta amarce da angonta Mohammed Mohammed Kala wadanda za a daura aurensu ranar Asabar 26 ga watan Nuwamban 2022 a Maiduguri.

A ‘yan lokutan nan dai ana yawan samun yin aure na Jaruman Kannywood lamarin da jama’a ke gani wata alama ce da Jaruman na Kannywood musamman Mata za su yi bankwana da Masana’antar zuwa gidan Aure.

Labarai Makamanta