Dukiyar Attajiri Dangote Ta Sake Hawa Sama

Labarin dake shigo mana yanzu haka na bayyana cewar Attajirin da ya fi kowa kudi a Afirka, Aliko Dangote, yana kan ganiyar sake lashe wannan mataki a shekarar, matsayin da ya lashe tun a shekarar 2014 wanda kuma zai zarce a karo na biyu a jere a sashinsa na siminti.

Tashin farashin hannun jarin kamfanin simintin Dangote da na man fetur da taki sun taimaka wajen bunkasa arzikinsa da ya kai dala biliyan 2.3 a bana zuwa dala biliyan 20.1 a ranar 3 ga watan Disamba, wanda ya kasance mafi arziki tun 2014, inji Bloomberg Bilionaires Index.

A cewar Bloomberg, tsananin bukatar siminti da hauhawar farashin kayayyakin gine-gine a Najeriya, sun taimaka wajen habaka kudaden shiga na kamfanin Simintin Dangote.

Kamfanin simintin Dangote shi ne babban kadaran da ya fi kowanne daraja a kayayyakin attajirin. Tun daga farkon shekarar 2021, darajar hannun jarin kamfanin simintin Dangote ya karu da kashi 24.49% daga N224.90 kan kowane kaso a ranar Litinin 4 ga watan Janairu zuwa N280 zuwa a ranar Juma’a 3 ga Disamba, 2021.

Simintin Dangote ba wai kamfani ne kawai mafi daraja a harkar hada-hadar Najeriya ba, yana daya daga cikin manyan masu daukar ma’aikata a kasar.

Bloomberg ya kuma lura cewa Dangote ya kuma shirya kammala wani aikin matatar mai da ta kai dalar Amurka biliyan 19 wacce za ta iya biyan fiye da bukatar man fetur a Najeriya.

Dangote, a bana, ya kuma fara fitar da taki zuwa kasashen Amurka da Brazil bayan kammala wani katafaren kamfanin da zai iya samar da ton miliyan 3 na nau’in takin urea da ammonia a duk shekara.

Labarai Makamanta