Duk Dan Bindigar Da Ya Yi Gigin Shiga Jihata Zai Bakunci Lahira – Gwamnan Kogi

Gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello, ya sha alwashin ɗaukar tsattsauran mataki kan Yan ta’addan Daji Matukar Suka Shigo Masa jiha..

Gwamna Bello ya yi wannan furucin ne yayin da ya karɓi bakuncin shugaban ƙaramar hukumar Yagba West, Pius Kolawole, domin tattaunawa kan fashi da makami a yankinsa da kuma matakan da aka ɗauka.

Gwamnan Ya ƙara jaddada kudirin gwamnatinsa na haɗa kai da dukkan hukumomin tsaro wajen tsaftace jihar daga mutane masu tunanin aikata ta’addanci ba tare da tausayi ba.

Labarai Makamanta