DSS Ta Saki Salihu Tanko Yakasai

Hukumar ‘yan sandan farin kaya DSS ta sako Salihu Tanko Yakasai Dawisu tsohon mai magana da yawun gwamnan Kano Dr Abdullahi Umar Ganduje.

Ɗan’uwan Salihu Yakasai, Umar, ne ya tabbatar wa manema labarai hakan a daren ranar Litinin.
” Hukumar DSS ta sako dan uwa na. Muna tare dashi haka a gida”
Ba tare da wani karin bayani game da sharrudan belin ba.

A daren ranar Asabar ne SSS ta amsa cewa ita ce ta kama Salihu Tanko Yakasai bayan jama’a sun dade suna cece-kuce kan batun a dandalin sada zumunta.

Shugaban hukumar ta SSS reshen jihar Kano, Alhassan Mohammed, da farko a safiyar ranar Asabar ya musanta cewa hukumar ne ta kama Tanko Yakasai, inda ya ce rahoton jita-jita ne kawai.

Amma cikin wata sanarwa da ya aike wa Daily Nigerian a daren ranar Asabar, kakakin hukumar, Peter Afunanya, ya tabbatar da zargin da ake yi da farko na cewa hukumar ce ta kama Salihu Tanko Dawisu.

Gabanin kama Yakasai, Gwamnan Kano Abdullahi Ganduje ya ce ya sallami shi ne saboda ‘furta maganganu’ da suka ci karo da tsarin jam’iyyar APC da gwamatin jihar da ya ke yi wa aiki.
A rahoton da muka samu na baya bayan nan, na bayyana cewar Lauyoyin Yakasai na neman bahasin kamun nashi a shari’ance.

Labarai Makamanta