DPO Ya Lashe Gasar Karatun Al-Kur’ani A Kano

Rahotanni daga Jihar Kano na bayyana cewar Shugaban ofishin ƴan sanda na ƙaramar hukumar Takai ya lashe gasar izu 60 ta karatun Al Kur’ani mai tsarki da aka rundunar ƴan sandan jihar Kano ta shirya.

DPO Mahi Ahmad Ali, ya zo na ɗaya ne a gasar ajin izu 60, inda ya samu kyaututuka da dama da suka hada da kuɗi da kyayyaki na amfanin yau da kullum.

Gasar wacce aka kammala a ranar Alhamis ita ce irin ta farko da rundunar ƴan sandan Kano ta gudanar ga jami’nta.

Ƴan sanda kusan 39 ne suka shiga musabaƙar ta Al Kur’ani ta kwana biyu kuma wadanda suka shiga musabaƙar sun samu kyaututuka daban daban.

Kakakin rundunar ƴan sandan Kano Abdullahi Haruna Kiyawa ya ce gasar ta ƴan sanda ce zalla kuma gasar ta ƙunshi izu biyu da izu biyar da 10 zuwa 20 da masu izu 40 da 60

Sai dai gasar ta maza ce zalla ba mata amma rundunar yan sandan Kano ta ce saboda wannan ne karon farko, tana fatan a gaba za a ƙara shiri.

SP Mahi Ahmad Ali shugaban ƴan sanda mai kula da ƙaramar hukumar Takai da ke Kano shi ne wanda ya lashe gasar Al Kurani ta izifi 60.

Bayan lashe gasar ya yi godiya ga Allah inda ya ce wannan wata dama ce ta ƙara inganta karatunsa na Al Kur’ani.

“Aikinsa na ƴan sanda bai hana ni tilawar Kur’ani ba,” in ji shi.

Kadif Abubakar Abdullahi Usman daga kwalejin ƴan sanda ta Wudil ne ya zo na biyu a karatun izu 60 yayin da sufeto Ibrahim Abubakar da ke aiki a hedikwatar yan sanda da ke Bompai ya zo na uku.

Labarai Makamanta