Domin Kare Kai Na Buƙaci Makiyaya Su Rinƙa Yawo Da Manyan Makamai

Gwamnatin jihar Bauchi ƙarƙashin jagorancin Gwamnan Jihar Ƙauran Bauchi ta kara haske a kan jawabin Gwamna Bala Mohammed inda yace makiyaya su dinga yawo da Manyan Bindigogi ƙirar AK-47 domin ba kansu kariya.

A wata takarda da aka fitar a ranar Lahadi 14 ga watan Fabrairu, Mukhtar Gidado wanda babban mai ba gwamnan shawara ne a kafafen sada zumunta ya ce ba a fahimci tsokacin ubangidansa bane, ko kaɗan maganarshi ba tana nufin tayar da hankali ban sai dai kawai neman mafita ta kare kai ga Fulani.

Idan za a tuna, Gwamna Bala Mohammed na jihar Bauchi ya bukaci makiyaya su dinga yawo da AK-47 domin shawo kan matsalar satar shanunsu da ake yi.

Amma a martanin da gwamnan yayi, Gidado ya ce ba a fahimce shi bane kuma ba yana nufin goyon bayan ‘yan ta’addan makiyaya bane.

“Gwamnan zai so a gane cewa yana so ne ya janyo hankalin masu ruwa da tsaki da su yi kokarin hana hauhawar rikici kamar dai yadda duk wani mai kishin kasa zai yi.

A kuma gujewa duk wani hari da zai iya jefa kasar nan cikin halin rikici.”

Labarai Makamanta