Dole Musulmi Su Kafa Ta Su Majalisar Dinkin Duniya – Erdogan

Shugaban ƙasar Turkiyya Recep Tayyib Erdogan, ya bayyana cewa tunda majalissar ɗinkin duniya, ba za ta iya share hawayen ƙasashen Musulmin duniya ba to bata da amfani suci gaba da zama a cikinta, duba da yadda ake ta hallaka musulmin ƙasar Palasɗinawa, wanda Isra’ila ke yi amma ba tare da majalissar ɗinkin duniya ta ɗauki wani mataki na hana faruwar hakan ba.

Erdogan ya ce, “ya zama wajibi mu kafa sabuwar majalissar ɗinkin duniya ta Musulunci (Muslim United Nations) domin kuwa abubuwan da ake yi na kisan musulmi tare da aibata su da sunan ƴan ta’adda hakan ba abun da zamu kyale bane, in ji shi, a wani jawabi da yayi a daren jiya a kafar talabijin ɗin kasar.

Muna fatan Allah ya taimaki wannan bawa na sa dake son kare addinin Musulunci da Musulmi, amin.

Labarai Makamanta