Dole Gwamnati Ta Samar Da Dokar Ƙayyade Haihuwa Ga ‘Yan Najeriya – Sunusi

Tsohon Sarkin Kano, Malam Muhammad Sanusi II yayi kira da babbar murya ga gwamnati da ta saka tsauraran dokoki da za su daidaita hauhawar yawan jama’a a kasar nan, domin shawo kan matsalar talauci dake addabar kasar musamman yankin Arewacin Kasar.

Sanusi wanda yayi magana a ranar Laraba yayin wani taro a Legas, ya ce ya dace jama’a su dinga haifar ‘ya’yan da za su iya kula da su, ba wai tara yara rututu ba a sake su bisa tituna kamar Awaki, kamar yadda jama’ar Arewa musamman Hausawa ke yi ba.

Tsigaggen Sarkin na Kano wanda masanin tattalin arziki ne kuma Tsohon gwamnan babban bankin Najeriya yace, abubuwan da ke bayyana a halin yanzu sun nuna cewa gwamnati ba za ta iya samar da dukkan ababen more rayuwa da ake bukata ba, ga ‘yan Najeriya ashe ya zama dole a taka wa abin birki.

Sanusi ya kushe yadda ake haihuwa a kasar nan ba tare da karfin kula da yaran ba, wanda yace hakan ba daidai bane a tsarin karantarwar addinin Musulunci.

“Yadda jama’a ke auren duk yawan matan da suke so ba tare da wata dokar da ta gindaya yawan yaran da za a haifa ba bai dace ba ko a Musulunci.

“Ban san dalili ba amma akwai doka a Musulunci da ta hana tara iyali ba tare da kayyade su ba. Babu wani tabbacin cewa za a iya kula dasu sannan an tara su an yi watsi da dawainiyarsu.

Labarai Makamanta