Dokar Zabe: Buhari Ya Bukaci A Goge Sashen Masu Mukaman Siyasa Su Sauka Kafin Zabe

Rahotanni daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya buƙaci Majalisun Dokokin ƙasar su goge sashen da ya hana masu muƙaman siyasa neman takara a cikin sabuwar dokar zaɓen da ya sanya wa hannu a ranar Juma’a.

Shugaban ya bayyana hakan ne yayin da yake sanya wa dokar hannu a fadarsa da ke Abuja.

Sashe na 84 (12) na Dokar Zaɓe ta 2022 ya buƙaci duk wani mai muƙamin siyasa ya ajiye muƙaminsa kafin ya tsaya wata takara a babban zaɓe.

Hakan na nufin za a tilasta wa wasu manyan ƙusoshin gwamnatin ta Buhari su sauka daga muƙamansu kafin babban zaɓe na 2023.

Buhari ya ce wasu daga cikin tanadin dokar za su haɓaka harkokin zaɓe “kamar 3, 9(2), 34, 41, 47, 84(9), (10), (11) da sauransu”.

“Sai dai abin ba haka yake ba… a sashe na 84 (12) wanda ya shatale masu riƙe da muƙaman siyasa game da zaɓensu da kuma jefa musu ƙuri’a a manyan tarukan jam’iyyu idan ba a gudanar da zaɓen ba cikin kwana 30 kafin zaɓe,” in ji shugaban.

Labarai Makamanta

Leave a Reply