A ranar Litinin 9 ga watan Janairun 2023 ne sabuwar dokar takaita cire kudi ta fara aiki a Najeriya tun bayan da aka bayyana sanya ta a shekarar da ta gabata.
Babban Bankin Najeriya (CBN) ya bayyana a baya cewa, ya kirkiri hanyar rage yawaitar yawon kudade a hannun jama’a domin tabbatar da ana amfani da hanyoyin biya daban-daban.
A dokar da CBN ya sanya, ya ce daidaikun mutane za su iya cire N500,000 ne a mako a bankuna ko injunan ciren kudi na ATM.
Hakazalika, an ba kamfanoni damar cire kudaden da suka kai N5,000,000 a cikin mako duk dai don a rage yawon kudi a Tarayyar Najeriya.
Babban bankin ya ba da mafita ga duk wanda ke son cire kudi fiye da adadin da aka shar’anta a sama. Ga daidaikun mutanen da ke son cire sama da N500,000, banki zai caji akalla 5% na adadin da za a cire. Hakazalika, ga kamfanoni, duk mai son cire sama da N5,000,000, to tabbas zai ba da 10% na adadin da yake son cirewa ga banki.
You must log in to post a comment.