Dogaro Da Kai: An Horar Da Mata Sana’o’i A Adamawa

Domin ganin an magance matsalar rashin aikin yi a tsakanin mata da matasa an horar da mata sana’oi daban daban a jihar Adamawa.

Horarwas dai ta gudana ne karkashin kungiyar kirkiro aikin yi ga yan Africa wanda kuma an dauki tsawon watanni biyu ana gudanar da horon a Yola.

Da yake gabatar da jawabi a wurin bikin kammala horon kwamishinan koyar da kananan sana’o’i a jihar Adamawa Iliya James wanda Kefas Yunusa ya wakilta yace koyon sana’a abu ne da yake da mutukan muhimmanci ga dan Adam don haka ya kamata Al umma musammanma matasa da su maida hankali wajen koyon sana’ar digaro da kai domin ganin an samu cigaba dama bunkasa tattalin Arzikin jiha da kasa baki daya.

Shima a jawabinsa Alhaji Usman Abubakar wanda akafi sani da Manu Ngurore jan hankalin wadanda suka amfana da shirin yayi da su kasance masu yin amfani da abunda aka koya musu ta hanyar da ta dace wanda a cewarsa hakan zai taimaka wajen bunkasa aikin yi a tsakanin al’umma baki daya.

Anashi bangaren Shehu Ahmed wanda ya wakilci dan majalisa mai wakiltar karamar Hukumar Yola ta Arewa a majalisar dokokin jihar Adamawa wato Hamidu Sajo Lekki yace a shirye yake ya taimaka da dukkanin abinda ya kamata domin ganin an samu saukin rayuwa a tsakanin Jama a.

Solomon Nuhu yace zasu cigaba da yin irin wadannan aiyuka wanda a cewarsa bukatarsu itace ganin kowa ya samu sana’ar dogaro da kai ba sai an dogara da gwamnati ba.

Wasu mata daga cikin wadanda suka samu horon sun shaidawa muryar yanci farin cikinsu dama jin dadinsu dangane da wannan horo da akayi musu.

Cikin horon da akayi wa matan dai sun hada da koyon dinki, da takalma, Jaka, da dai sauransu.

Labarai Makamanta