Labarin dake shigo mana daga Fadar Shugaban Ƙasa dake Abuja na bayyana cewar, Shugaba Muhammadu Buhari ya isa birnin Paris na Faransa, a wata ziyara ta kwana ɗaya, kamar yadda wata sanarwa daga fadarsa ta bayyana.
Mai taimaka wa shugaban kan yaɗa labarai Femi Adesina a sanarwar ya ce shugaban ya kai ziyarar ne bisa gayyatar da Shugaba Emmanuel Macron ya yi masa.
Buhari dai ya yi ƙaurin suna wajen yawan yin tafiye-tafiye zuwa kasashen waje, lamarin da jama’ar ƙasar da dama ke ƙorafi akai.
You must log in to post a comment.