Daukakata A Fim Daga Allah Ne – Jaruma Amal Umar


Fitacciyar Jaruma a Masana’antar fina-finai ta kannywwod mai suna Amal Umar, ta bayyana daukakar da Allah ya ba ta, da cewa wani Abu ne da Allah ne kawai ya tsara hakan.

Jarumar ta bayyana Hakan ne a lokacin tattaunawarta da Jaridar Dimukaradiyya a ranar Alhamis.

“Da farko lokacin da na shigo harkar fim ban yi zaton zan samu daukaka da wuri ba, Amma cikin ikon Allah, a karamin lokaci Allah ya daukaka Ni na zama Fitacciyar jaruma ta yadda har na zamo abin kwatance”

Amal ta ce “Yanzu babu abun da zan ce sai godiya ga Allah, domin kuwa a yanzu duk in da na je a cikin taro za a ce Amal ce, Kuma hakan ya ba Ni damar yin mu’amala da mutanen da ban zata zan Kai ga hakan ba, don haka daukaka a gare Ni ta zo mini a ba zata, sai godiya ga Allah.”

Daga karshe ta yi fatan gamawa da harkar fim lafiya, kuma idan ta samu miji ta yi aure.

Labarai Makamanta