Daukakata A Fim Daga Allah Ne – Azeema Gidan Badamasi

Jarumar Kannywood mai tashe, Hauwan Ayawan wacce aka fi sani a matsayin Azeema a cikin shiri mai dogon zango na tashar Arewa24 wato ‘Gidan Badamasi’ ta yi bayani kan yadda ta shahara a lokaci guda a masana’antar.

A cikin wata hira da Daily Trust ta yi da ita, jarumar haifaffiyar jihar Kaduna ta bayyana cewa bata taɓa sanin cewa wata rana za ta shahara haka ba duk da cewar ta taso da sha’awar yin fim tun tana yarinya.

Jarumar ta yi godiya ga Allah kan wannan mataki da ya kai ta a masana’antar domin a cewarta bata taba tunanin cikin dan kankanin lokaci za ta kai inda ta kai ba a yanzu.

“Sunana Hauwa Ayawa kuma an fi sanina da Azeema a masana’antar shirya fim. Wannan suna ne da na samu sakamakon rawar ganin da na taka a shiri mai dogon zango na ‘Gidan Badamasi’ wanda ake nunawa a tashar Arewa24.

“An haife ni a Kaduna ta arewa, jihar Kaduna. Na yi makarantar Firamare a jihar Kaduna. Sannan na tafi makarantar sakandare ta mata, GGUSSS Kwatarkwashi a jihar Zamfara sannan daga baya na halarci makarantar sanin ilimin na’ura mai kwakwalwa.Sai dai, ina da niyar ci gaba da karatun jami’a.”

“Na dade ina da sha’awar yin fim saboda furodusa ce ta haife ni. Na taso ina ganin yan fim a gidanmu. An hada ni da daya daga cikin manyan daraktoci a masana’antar Muhammed Alfa Zazi wanda daga bisani ya sanyani a harkar fim a Kannywood sannan tun daga lokacin nake taka rawar gani.

“Kuma a wurin daukar wani fim ne na hadu da daraktan fim din ‘Gidan Badamasi’ Falalu Dorayi, wanda ya lura da yadda nake taka rawar gani sannan ya nemi ya saka ni a wani shiri mai dogon zango. Yadda aka yi na samu gurbin Azeema kenan a ‘Gidan Badamasi.”

Kan halin da ta tsinci kanta a wajen daukar fim a ranarta ta farko, Azeema ta ce: “Gaskiya, na bai wa abokan sana’ata da dama mamaki saboda duk sun zata na saba yin fim ne. an fada mani cewa na yi kokari sosai kamar na dade ina fim, hatta daraktan fim din sai da ya jinjina ma kokarina.

Ban ji fargaba ba kamar wasu; na yi kokarin daidaita kai saboda na rigada na san yadda ake yi kuma cikin sa’a, na yi komai daidai.”

“Fim dina na farko sunansa ‘Musaddiq’, Mustapha M Sharif ne ya shirya fim din kuma wannan ne ya fara bani gurbi a fim din ‘Karar Kwana’. Fim ne da ya sa ni farin ciki, saboda an bani dama duk da manyan sunaye da ke cikin fim kuma wannan ne ya ba daraktoci da dama karfin gwiwa a kaina.”

Ta kuma bayyana cewa ta fito a cikin fina-finai akalla 25 kuma tana kan yi. Game da ko ta gamsu da abun da take ji daga yan kallo kan rawarganin da take takawa, Hauwa ta ce: “Tabbass na gamsu kuma burina ya cika.

“Kun gani, Ban dade a masana’antar fim ba amma Allah abun godiya, na kai matakin da ban taba tunanin zan kai ba a cikin dan kankanin lokaci kamar haka. Idan zan fadi, ban taba sanin cewa zan shahara haka ba cikin dan kankanin lokaci, Allah abin godiya!”

Labarai Makamanta