Dattawan Arewa Sun Yi Allah Wadai Da Kisan Hanifa

Rahotanni daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Kungiyar tuntuba ta Dattawan arewa wato ACF ta yi Allah wadai da mutuwar Hanifa Abubakar, yarinya yar shekara biyar da ake zargin wani shugaban makaranta da kashe ta a jihar Kano.

An yi garkuwa da dalibar a watan Disambar 2021 sannan wadanda suka sace ta suka nemi a biya naira miliyan 6 a matsayin kudin fansa. Yan sanda a Kano sun kama Abdulmalik Tanko, shugaban makarantar su Hanifa wanda ake zargi da kashe ta a ranar Alhamis.

A cewar sanarwa da kakakin kungiyar, Emmanuel Yawe, ACF ya fitar ranar Asabar Ƙungiyar ta yi kira ga gwamnati a dukkan matakai da su dauki matakan gaggawa domin kawar da illolin da ke addabar al’umma da aikata laifuka a makarantun kasar.

“Kungiyar tuntuba ta Arewa tana fatan nuna kaduwarta da rashin jin dadinta kan ayyukan ta’asar da ke gudana a makarantun Najeriya. “Wadannan sun hada da cin zarafi, kisa, garkuwa da mutane, luwadi, kungiyar asiri da sauransu.

Na baya-bayan nan shine zargin garkuwa da kisan daliba yar shekaru biyar, Hanifa Abubakar da malaminta Abdulmalik Muhammed ya yi a wata makarantar kudi da ke Kwanar Dakata a jihar Kano.

“Wannan labari ne mai ban tsoro kwatankwacin abin da ya faru a watan Disambar shekarar da ta gabata lokacin da dabilai yan uwan Sylvester Oromoni mai shekara 12 a Kwalejin Dowen, suka ci zarafinsa sannan suka azabtar da shi har lahira saboda ya ki shiga cikin ayyukansu na kungiyar asiri.

“Kungiyar tuntuba ta Arewa tana son jawo hankalin hukumomi kan wannan sabuwar annoba ta muggan kwayoyi, ta’addanci, kungiyoyin asiri da kuma mace-mace da ke gudana a fadin makarantun kasar da kuma jefa rayuwar ‘ya’yanmu mata da maza cikin hatsari.

“Wadannan abun tsaro ba su tsaya a iya makarantun kudi ba kawai. Amma mun fi mayar da hankali kan abubuwan da ke wakana a makarantun kudi saboda suna daukar dalibansu tamkar abun da ake siya da kudi ne.

“Wannan mummunar dabi’a ce da ba iya makomar wadannan yaran za ta bata ba harma da Najeriya. Muna kira ga gwamnatocinmu da su shiga lamarin da karfi tare sannan su kawar da wannan yanayi.”

Labarai Makamanta