Dattawan Arewa Sun Soki Gwamnan Babban Banki Da Nuna Wariya

Kungiyar tuntuba ta magabatan Arewa Arewa Consultative Forum (ACF) ta rubuta wasika zuwa ga gwamnan babban bankin Najeriya CBN, Godwin Emefiele, inda take zargin shi da nuna wariya ga yankin.

Kungiyar Dattawan Arewan ta koka wa gwamnan CBN a kan yadda ake ware jihohin Arewa wajen yin rabon tsare-tsaren tattalin arziki a Najeriya, sannan ake fifita Jihohin Kudu duk da yawan jama’a da yankin Arewan ke dashi.

Shugaban Kungiyar Dattawan na kasa, Mista Audu Ogbeh ne ya sa hannu a wannan doguwar wasika da kungiyar ta aika wa Gwamnan babban bankin.

Dattijo Audu Ogbeh ya ce babu adalci, kuma ba a kyauta wa yankin Arewa a rabon da ake yi duk da cewa yankin ne ya fi kowane bangare yawan jama’a a fadin kasar.

Tsohon Ministan gonan ya koka da cewa mutanen da ke zaune a karkara a yankin Arewa ba za su ci amfanin manufofin babban bankin kasar yadda ya kamata ba.

“Ba a duba kananan bankuna wadanda su ne ya kamata su amfani mafi yawan al’ummar kasaar nan.” “Wani sabon karamin banki guda wanda yake hannun gwamnati ne CBN ya ke tanka wa, ya raba kudin tallafi da shi, ana watsi da sauran kananan bankuna masu rajista.”

Wasikar dattawan Arewa ta kara da cewa: “Sauran kananan bankuna sai sun fita sun nemo kudi da tsada, sannan su yi takara da sauran bankunan da babban bankin ke fifita wa.

Dattijo Audu Ogbeh ya kuma yi kaca-kaca da sabon sharadin da aka kawo wajen bude karamin banki, ya ce za a kori da-dama daga cikin bankuna 310 da ake da su a kaf Arewa.

Labarai Makamanta