Dattawan Arewa Sun La’anci Kisan Da Ake Yi Wa ‘Yan Arewa A Kudu

Kungiyar Dattawan Arewa ta bayyana matukar damuwarta kan yadda ake ta samun yawaitar batanci da kashe-kashen ‘yan Arewa a Kudancin Najeriya, musamman Kudu maso Gabas.

Daraktan yaɗa labarai da bayar da shawarwari na kungiyar Dr Hakeem Baba-Ahmed ne ya bayyana matsayin kungiyar a cikin wata sanarwa a jiya.

Kungiyar Dattawa ta ce, Kisan da aka yi wa ‘yan kasar Nijar kwanan nan a Jihar Imo, anyi shine bisa tunanin yan yankin Arewa ne.

Sanarwar yay kara da cewa da alama kungiyoyin da ke kai wa ‘yan Arewa hari suna samun kwarin guiwa ne daga shirun shugabanni da rashin daukar matakan da suka dace daga jami’an tsaro. Kungiyar ta sake jawo hankalin jama’a kan illolin da ke tattare da kara ta’azzara al’amura da tada hankali.

Daga karshe kungiyar ta bukaci gwamnati, al’umma da jami’an tsaro suka kara kaimi wajen kare rayuka da dukiyoyin yan Arewa.

Labarai Makamanta