Labarin dake shigo mana daga Jihar Kaduna na bayyana cewar Kungiyar Dattawan Arewa (NEF), a ranar Litinin, 29 ga watan Nuwamba, ta bukaci shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya yi watsi da bukatar wasu fitattun shugabannin Igbo, inda suka bukaci a sako Nnamdi Kanu, shugaban ‘yan awaren IPOB.
Kungiyar ta bayyana cewa babu wani dalili na aminci, ingantacce ko kuma sanin makamar amincewa da bukatar, kuma ta shawarci shugaban kasa da kada ya jinkirta bayyana cewa za a bar tsarin shari’a yayi aikinsa akan Kanu.
Dattawan sun bayyana haka ne a cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun mai magana da yawun ta, Dr. Hakeem Baba-Ahmed, kuma aka rarraba ta ga manema labarai.
“Kungiyar Dattawan Arewa ta yi nazari sosai kan bukatar da dattawan Igbo suka yi wa shugaban kasa Muhammadu Buhari na ya kawo karshen shari’ar da ake yi da Nnamdi Kanu kuma a sake shi ba tare da wani sharadi ba.
“Har ila yau, ta lura da martanin da shugaba Buhari ya bayar wanda dukkansu sun tabo muhimman batutuwan da suka shafi bukatar, da kuma jajircewarsa na yin la’akari da hakan.
“Kungiyar ta ba da shawarar cewa shugaba Buhari zai yi wa kasar rauni wanda tuni ta fuskanci barazanar kalubalen tsaro da yankinta idan ya jinkirta bayyana matakin da ya dace, wanda shi ne a bar tsarin shari’a yayi aikinsa kan Kanu.”
You must log in to post a comment.