Dangote Ya Haye Martaba Ta Farko Na Wanda Ya Fi Kowa Arziki A Afirka

Hamshakin mai kudin Najeriya kuma Bakano, shugaban kamfanin Dangote Group, Alhaji Aliko Dangote, ne mutum mafi arziki a nahiyar Afrika a shekarar 2020.

Rahoton Forbes. Wannan shine karo na tara a jere da attajirin ya zarcewa dukkan masu halin nahiyar. Jerin masu kudin ya mayar da hankali kan kasashen Afrika takwas masu kudi; yayinda kasar Masar da Afrika ta kudu suke da masu kudi biyar-biyar a jerin, Najeriya na da hudu, sannan kasar Maroko mai biyu.

Rahoton ya bayyana cewa Alhaji Aliko Dangote ya zo na daya da arzikin dala bilyan goma ($10.1 billion) na kasuwancinsa a Siminti, man fetur, flawa, Timatur da Sukari, sai Nassef Sawiris na kasar Masar mai arziki dala bilyan takwas ($8 billion) ya zo na biyu, sai Mike Adenuga mai kamfanin sadarwan Glo ya zo na uku.

‘Yan Najeriyan da suka shiga jerin masu kudin nahiyar sabanin Dangote sune Abdus Samad Isyaka Rabiu, Mike Adenuga, da Folorunsho Alakija.

1- Aliko Dangote $10.1 billion.

2- Nassef Sawiris $8 billion

3- Mike Adenuga $7.7 billion

4-Nicky Oppenheimer $7.7 billion

5- Johann Rupert $6.5 billion

6-Issad Rebrab $4.4 billion

7- Mohamed Mansour $3.3 billion

8-Abdulsamad Rabiu $3.1 billion

9-Naguib Sawiris $3 billion

10-Patrice Motsepe $2.6 billion

11-Koos Bekker – $2.5 billion

12- Yasseen Mansour – $2.3 billion

13- Isabel dos Santos – $2.2 billion

14- Youssef Mansour – $1.9 billion

15- Aziz Akhannouch – $1.7 billion

16- Mohammed Dewji – $1.6 billion

17- Othman Benjelloun – $1.4 billion

18- Michiel Le Roux – $1.3 billion

19- Strive Masiyiwa – $1.1 billion

20- Folorunsho Alakija – $1 billion

Related posts