Dangote Da MTN Ne Ke Sahun Gaba Wajen Biyan Haraji – Hukumar Tara Kudade

Kamfanin Simintin Dangote ya zama kamfanin da ya fi ko wanne kamfani biyan kudin haraji a Najeriya. Fittacen kamfanin mai kera siminti a Nigeria ya zama na farko cikin jerin kamfanoni 152 da hukumar kasuwanci ta Nigeria, NGX, ta lissafa a watanni shida na farkon 2021.

A cikin watanni 6 na farkon 2021, Kamfanin Simintin Dangote da wasu kamfanoni 13 da ke kasuwanci a NGX sun biya harajin N289.4b ga hukumar FIRS da wasu hukumomin da ke samarwa gwamnati kudin shiga.

Kamfanin Simintin Dangote ya biya gwamnatin tarayya zunzurutun kudi Naira biliyan 89.62, an samu karin 144% kan abinda kamfanin ya biya na N36.71bn a shekarar 2020.

Sauran kididdigar sun nuna Kamfanin MTN Nigeria wanda ya zama kamfani na 2 a biyan haraji, ya samar da Naira Biliyan 73.29 a H1 2021, wanda ya zama karin kaso 64% daga Naira biliyan 44.69 da aka ruwaito a H1 2020.

Yayin da bankin United Bank for Africa ya biya harajin Naira Biliyan 15.06 daga Naira Biliyan 12.7 da ya biya. Guaranty Trust Holding Co PLC, duk da cewa shi ya zo na uku ya biya Naira Biliyan 13.64 a H1 2021, hakan na nufin an samu ragin 12% daga Naira Biliyan 15.44 da ya biya a H1 2020.

An samu bayanai a kan yadda Access Bank ya biya harajin Naira Biliyan 10.56 a H1 2020 daga Naira Biliyan 13.27 a H1 2020. Zenith Bank Plc ya biya harajin Naira Biliyan 10.94 a H1 2020, karin 6.2% daga Naira Biliyan 10.3 a H1 2020.

A dayan bangaren kuwa, akwai FBN Holdings da ya biya harajin Naira biliyan 7.15 a H1 2020 karin 24% akan Naira biliyan 5.77 a H1 2020. Nestle Nigeria Plc sun biya harajin Naira Biliyan 11.65 a H1 2020 a bangaren kayan amfanin jama’a masu saurin shiga (FCMG), ragin 3.2% daga Naira biliyan 12.04 da aka ruwaito a H1 2021.

An amshi harajin Nigerian Breweries Plc da Guinness Nigeria Plc a H1 2021 na Naira Biliyan 4.2 da 4.5 kowanne.

Labarai Makamanta