Damfarar Da Aka Yi Mini Ce Ta Sa Nayi Tunanin Kashe Kaina – Ummi Zeezee

Ummi Zeezee ta bayyana cewa wani dan Neja Delta ne ya damfare ta naira miliyan 450 da ta bashi su yi wani harkar siye da siyarwar danyen mai.

A hira ta da tayi da VOA Zeezee ta ce wani ne ya damfare ta kudinta har naira miliyan 450.

” Mun shirya zamu yi sana’ar siyar da danyen mai ne. Na tattara kudi na masu yawa har naira miliyan 450, na bashi. Kawai na wayi gari ne ya waske da kudin, babu shi ba bu dalilin sa.

Na yi kokarin neman sa amma ban san inda ya ke ba sannan ya cire ni daga abokansa a shafukan sa na sada zumunta a yanar gizo.

Zee ta kara da cewa wannan abu shine ya tada mata da hankali ya saka ta cikin hali na damuwa da ta ji kamar ta kashe kanta.

Da aka tambaye ta ko wani irin sana’a ta ke yi yanzu, tace gwamnoni ke bata kwangilolin hanyoyi a jihohi sannan kuma tana harkar mai. Yanzu kuma tana harkar siyar da danyen mai ne, wanda a ciki ne aka damfare ta naira miliyan 450.

Idan ba a manta ba, Ummi Zeezee ta rubuta a shafinta na Instagram ranar Asabar cewa ita fa rayuwar ya ishe ta, ta gaji sanna ta shiga wani hali na damuwa da take ji kamar ta kashe kanta.

“A ‘yan kwanakin nan, na shiga matsanancin kuncin rayuwa, ta yadda har na kan ji ina so na kashe kaina.”

Labarai Makamanta