Dama Ga Matasa: Ma’aikatar Gona Zata Ɗauki Ma’aikata

Ma’aikatar gona (Federal Ministry of Agriculture) ta bude wani shafi da neman masu Diploma, Babbar Diploma da Degree don a dauki mutum 2000 a kowacce karamar hukuma a saka su a wani tsari na Buhari Young Farmers Network.

Wanda suka karanci kimiya (science) da kuma ilimin sarrafa na’ura mai kwakwalwa (computer) zasu samu babban matsayi a cikin wannan tsari. Wanda suka karanci sauran bangarori suma ba’a barsu a baya ba.

Kada mu bari a bar mu a baya, mu shiga mu gwada sa’armu, watanni baya haka a fito da tsarin bashi na bankin Nirsal amma mutane suka yi banza dashi, sai yanzu da aka ga wanda suka cike sun fara jin alert kowa ya rikice wai sai an yi masa alhalin an rufe.

Abunda ake bukata wajen cikewa shine:

Name
State
Local government
Phone number
Email
Passport photograph
Area of specialization

Za ku iya shiga wanan shafi ta

https://www.nalda.ng
Idan ka cike zaka jira a fitar da sunayen wanda sukayi nasara. Amma yana da kyau kayi likin kayi sharing ko da kai ba zakayi applying ba, don ka taimakawa wani a abokanka.

A yada ko a samu a taimaki wasu, kada mu bari nan gaba kuma zai yi amfani.

Labarai Makamanta