Dalilinmu Na Kin Janye Tallafin Fetur – Fadar Shugaban Kasa


Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya ce abin da ya sa bai cire tallafin man fetur ba shi ne don gudun tsananta wa al’ummar ƙasar.

Shugaban ya fadi hakan ne a wata hira ta musamman da ya yi da jaridar Bloomberg ta intanet ta Amurka da aka wallafa a ranar Talata.

Bloomberg ta tambayi Buhari cewa me ya sa ya ƙi amsa kiraye-kirayen da Asusun ba da lamuni na duniya IMF, da Babban Bankin Duniya ke masa tsawon shekaru na ya janye tallafin fetur kuma canjin kuɗaɗen ƙasashen waje su zama na bai ɗaya?

Sai ya amsa da cewa har yanzu akwai ƙasashen yammacin duniya da ke bin tsarin biyan tallafin fetur.

“To me ya sa za mu janye namu a yanzu?

“Abin da ƙasashen waje ke fama da shi shi ne sun fi mayar da hankali kan tsare-tsaren da aka yi a rubuce amma suna mantawa da tasirin haka ga al’ummominsu,” in ji shi.

A bara ne gwamnatin Shugaba Buhari ta so janye tallafin mai, “amma bayan tuntuɓar masu ruwa da tsaki da yadda abubuwa suka kasance a bana, ɗaukar matakin ba mai yiwuwa ba ne.

Sai dai ya ce ƙara samar da albarkatun fetur a cikin ƙasar ta hanyar sababbin matatun mai da ake sa ran za su fara aiki nan gaba a wannan shekarar za su taimaka sosai.

Kan batun tsadar kuɗaɗen ƙasashen waje da mayar da farashinsu na bai ɗaya kuma shugaban Najeriyar ya ce hakan na faruwa ne sakamakon wasu abubuwa da ke faruwa a wajen kasar.

“Idan aka ci gaba da samar da mai a cikin gida da tsare-tsaren samar da abinci, za a samu a daidaita farashin kuɗaɗen da mayar da su bai 

Labarai Makamanta