Rahotannin dake shigo mana daga Gusau fadar Gwamnatin Jíhar Zamfara na bayyana Tashar Trust TV ta zanta da kasurgumin jagoran ‘yan bindiga Bello Turji, inda ya bayyana dalilin da yasa ya dau bindiga ya fara ta’addanci.
A cewarsa, rashin adalcin da akewa Fulani Makiyaya da wulaƙanta su tare da mayar dasu Saniyar ware cikin al’umma ya tilasta masa daukar bindiga domin ɗaukar fansa.
A hirar, ya bayyana cewa a kasuwar Shinkafi ya fara ganin yadda aka yiwa dan Adam yankan rago. Yace jami’an Yan Sa Kai suka kawo wani mutumi Bafillace kusa da kwatan Shinkafi kuma suka yi masa yankan rago a bainar jama’a.
Bello Turji yace dole tasa makiyaya suka fara daukar bindiga don kare kawunansu saboda an hanasu shiga garin Shinkafi a jihar Zamfara.
You must log in to post a comment.