Dalilina Na Watsi Da Kujerar Mataimakin Shugaban Kasa – Zulum

Labarin dake shigo mana daga Maiduguri babban birnin jihar Borno na bayyana cewar Gwamnan Babagana Umara Zulum ya lashe zaben fidda gwanin jihar da aka yi, ya kuma yi watsi da masu yi masa ta yin ya nemi mataimakin shugaban Najeriya.

Babagana wanda shi kadai ne dan takarar a karkashin jam’iyyar APC ya lashe zaben ba tare da hamayya ba, wanda hakan zai ba shi damar karawa da takwarorinsa na sauran jam’iyyun a zaben 2023.

An yi zaben fidda gwanin ne a cibiyar wasanni ta El-Kanemi da ke Maiduguri a yammacin Alhamis, kuma manyan ‘yan jam’iyyar APC sun halarci zaman ciki har da tsofaffin gwamnonin jihar da suka hada da Kashim Shettima da Ali Modu Sheriff da kuma Maina Ma’aji Lawan.

Ministan noma Mustapha Baba Shehuri da tsohon dan majalisar dattijai kuma Ambasadan Najeriya a China Baba Ahmed Jidda duk suna cikin mahalarta taron.

Labarai Makamanta