Dalilina Na Kwace Filin Jami’ar Ahmadu Bello – El Rufa’i

Rahotannin dake shigo mana daga Jihar Kaduna na bayyana cewar Gwamnatin Jihar karkashin jagorancin gwamna Nasiru El Rufa’i ta bayyana dalilinta na kwace fiye da hekta 74 a cikin filin Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zaria, ABU mai girman hekta 338.

A cewar gwamnatin, jami’ar ta sauya takardun mallakar filin ba bisa ka’ida ba, wanda ya ci karo da asalin takardun da gwamnati ta bayar.

Gwamnatin jihar ta ce asali tun 1965 aka bayar da takardun ga Northern Veterinary Experimental Station wacce ta koma Kwalejin kimiyar noma da kiwo ta ABU, wadanda daga bisani aka rarraba ba bisa ka’ida ba. Sannan an sayar da hekta 81 na cikin filin zuwa filoti 900 ba bisa ka’ida ba, yayin da aka gyara filoti 426 wadanda aka yi gine-gine daban-daban.

Yayin da manema labarai suka kai ziyara filin da ake rigima akan shi wanda yake Mando, karamar hukumar Igabi da ke Jihar Kaduna, Darekta Janar na hukumar tsari da bunkasa birane ta Jihar Kaduna (KASUPDA), Malam Ismail Umaru Dikko, ya ce takardar mallakar filin mai lamba 1060, ta kwalejin kimiyar noma da kiwo, wanda aka yi amfani da hekta 47 don harkokin ilimi da muhallin malamai, sai kuma wasu hekta 34.5 don noma da kiwo.

An musanya wa jami’ar da wani fili na daban a karamar hukumar Igabi Dikko ya ce filin ya zama barazana ga tsaron gabadaya yankin, wanda haka ya sa ya zama wajibi a kara gyara da kuma bunkasa wurin kamar yadda dokar Kaduna Master Plan ta 2016 ta tanadar.

Ya ce don gudun a ci gaba da rarraba filin ba bisa ka’ida ba, gwamnatin jihar ta yanke hekta 74 wanda zata mayar gidaje, makabartu, kasuwanni da kuma asibitoci. Darekta Janar din na KASUPDA ya ce za a musanya wa kwalejin kimiyar noma da kiwon wani fili da ke Kangimi a karamar hukumar Igabi don ta yi amfani da shi wurin kiwo.

A cewar Dikko, ABU ta yi yunkurin yin kakagida inda ta katange fiye da yawan filin da aka ba ta, ta kara yawan shi fiye da kima.

Anata bangaren jami’ar ta zargi gwamnatin Jihar Kaduna da yunkurin kwace mata fili mai girman hekta 196.24 wanda ya ci karo da bayanin gwamnatin inda tace filin ya kai hekta 338.

Labarai Makamanta