Dalilin Rashin Ganina A Taron Raba Lambobin Da Buhari Ya Yi – Sheikh Rijiyar Lemu

Labarin dake shigo mana daga jihar Kano na bayyana cewar sanannen malamin addinin Musuluncin nan Sheikh Muhammad Sani Umar Rijiyar Lemu ya yi bayani a game da lambar girmamawa da gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari ta ba shi kwanan nan.

A wata hira da ya yi da BBC Hausa, Dr. Muhammad Sani Umar Rijiyar Lemu yace samun wannan lambar yabo ya nuna an yaba aikin da malamai suke yi, kuma abin farin ciki ne yin hakan.

Babban malamin yace sai a daren Litinin da kimanin karfe 11:30 ya samu labarin yana cikin wadanda gwamnatin tarayya za ta ba lambar karramawan. Babu wani jirgin sama da aka samu wanda zai je birnin tarayya Abuja daga garin Kano, har a samu halartar bikin a Aso Villa da karfe 9:00 na safiyar ranar.

Ganin haka, sai shehin ya zabi wani wanda yake Abuja ya karbi lambar girma a madadinsa.

Kwararren masanin hadisin ya fadawa BBC cewa wannan lambar girma da ya samu ya nuna ya kamata gwamnati ta rika kula da aikin da malamai suke yi. A jawabinsa, malamin yace samun shaidar OON kwarin gwiwa ne ga shi da ire-irensa wadanda suke aiki dare da rana domin rainon zuciyar Bayin Allah.

Labarai Makamanta