Dalilin Kotu Na Bada Umarnin Tura Shugaban EFCC Gidan Yari

Rahoton dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar wata babbar kotun tarayya ta samu shugaban hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta ƙasa EFCC Abdulrasheed Bawa da laifin saɓa wa umurnin kotu, a wani hukunci da ta yanke a 2018.

A hukuncin da ya yanke ranar Talata, mai shari’a Chizoba Oji ya ce hukumar ta EFCC ta ƙi aiwatar da wani hukuncin da kotu ta yanke a ranar 21 ga watan Nuwamban 2018, inda ta umurci hukumar da ta mayar wa wani mutum motarsa kirar Range Rover da kuɗi naira miliyan 40.

Kotun ta buƙaci da a tura shugaban hukumar ta EFCC gidan yari har sai ya wanke kansa daga laifin.

Haka nan kotun ta buƙaci sifeta janar na ƴan sandan Najeriya ya tabbatar an aiwatar da hukuncin.

Wanda hukuncin na shekarar 2018 ya buƙaci da a mayar wa kayan nasa ne ya shigar da ƙara, inda yake zargin hukumar da ƙin bin umurnin da kotu ta bayar a hukuncin na farko.

Labarai Makamanta