Dalilin Ficewata A Shirin Labarina – Nafisa Abdullahi

Tauraruwar fina-finan Kannywood, Nafisa Abdullahi, ta ce daga yanzu ba za ta ci gaba da fitowa a shirin nan mai dogon zango mai suna ‘Labarina’ ba.

A sakon da ta wallafa a shafinta na Intagram ranar Asabar da daddare, tauraruwar ta ce ta ji dadin rawar da ta taka a cikin shirin, sai dai ta ce ba za ta iya ci gaba da shi ba saboda wasu dalilai na kashin kanta.

Amma wasu majiyoyi sun tabbatar wa BBC Hausa cewa ta dauki matakin ne saboda rashin jituwar da aka samu tsakaninta da mai shirya shirin kuma shugaban kamfanin Saira Movies, Malam Aminu Saira.

Nafisa ita ce babbar tauraruwa a shirin na Labarina mai farin jini a tsakanin ‘yan kallo inda take taka rawa a matsayin Sumayya.

“Janyewata daga [shirin] a wannan lokaci ya faru ne saboda yawan da ayyuka suka yi mini, ganin cewa hakan ba zai ba ni damar zuwa a dauki shirin na ‘Labarina’ ba.

Ba kamar yadda ake tunani ba, aiki wajen daukar shirin ‘Labarina’ ya kasance wani abin jin dadi, na yi aiki a fayyace tare da masu daukar shirin, da furodusa da ma dukkan wadanda suka shiga wannan babban shiri, kuma ina cike da farin cikin ganin cewa zan bar shirin ba tare da wata tsana ga kowa ba,” a cewar tauraruwar.

Sai dai masu sharhi a masana’antar Kannywood na ganin fitar Nafisa daga cikin shirin zai yi matukar tasiri ganin cewa ta janye ne a yayin da ake kan wata gaɓa mai matukar muhimmanci.

Hasalima tun kafin wannan sanarwa da Nafisa ta fitar, masu bibiyar shirin sun kosa a bayyana musu yiwuwar ci gaba da taka rawarta ko akasin hakan, bayan da aka nuna an sace ta kuma aka rika jan-kafa wajen nuna halin da take ciki.

Labarai Makamanta