Dalilin Da Ya Sa Nake Wakokin Gargajiya – Fati Nijar


Fitacciyar Mawakiya Hajiya Binta Labaran, wadda aka fi sani da sunan Fati Nijar, ta bayyana irin yadda ta ke riko da al’adar Hausa a matsayin abu mai muhimmamci a gare ta.

Fati Nijar ta bayyana Hakan ne ga wakilin Dimukaradiyya a lokacin da ya ke tattaunawa da ita dangane da yanayin wakokin ta musamman a yanzu da ta fi mayar da hankali a Kan wakokin da su ka fi kama da tatsuniya, in da ta ke cewa.

‘To ni dai ka ga Bahaushiya ce Kuma Ina kishin yaren Hausa da al’adun Kasar hausa, don haka ne ma za ka ga wakokin da na ke yi na fi yin so ne kamar tatsuniya, don ka ga an kusan mantawa da taofaffin tatsuniyoyin mu na Kasar hausa, wanda Kuma a yanzu a na bukatar a dawo da su. Don haka ne za kusan wakokin da na ke yi su ke tafiya a salon tatsuniya. ”

Ta ci gaba da cewar” Yanzu idan ka duba Wakar Ala Gidigo Charafke, Dawo dawo duk Salo ne na tatsuniya, Kuma Alhamdulillahi, yadda su ka karbu mutane su na jin dadin irin salon wakar, saboda tasirin al’adun da ke ciki. ”

Daga karshe ta yi Kira ga Mawaka musamman ma na Kasar hausa da su rinka Gina wakokin sua a Kan kyawawan al’adun mu na Kasar Hausa.

Labarai Makamanta