Dalilin Da Ya Sa Na Rasa Sarautar Kano – Lamido Sanusi

Tsohon Sarkin Kano Malam Muhammadu Sanusi II ya yi magana a game da tunbuke shi da aka yi daga kan sarautar Kano, inda ya bayyana cewar kaddara ce wadda ta riga fata, kuma ba a yin fushi da hukuncin Ubangiji.

An ruwaito cewa tsohon Sarkin ya yi wannan furucin ne a yayin da ya yi bikin cika shekara 60 da haihuwa a gidanshi dake birnin Ikko.

Khalifan na darikar Tijjaniya a Najeriya, Malam Muhammadu Sanusi II ya ce dole ce tasa ya hakura da sarautar Kano bayan kusan shekara shida da ya yi yana mulkin Kanawa.

“Na nuna adawa ga gwamnatin jiha ta a lokacin da ta nemi ta karbo aron Dala $1.8bn domin aikin jirgin kasa mai daukar mutane, a lokacin da ake da dinbin yara da ba su zuwa makaranta, kuma mu na fama da yunwa.”

“Na kuma yi kira ayi zaben gaskiya da gaskiya, na ba mutane shawarar su zabi ‘yan takara masu amana da kishi, wadanda za su iya aikin da aka ba su.” “A wurina, wannan shi ne aikina a matsayin Sarki.

Ban san ko wadannan suka jawo aka fara hari na ba, amma na san babu wanda zai wuce kaddara.” “Idan Ubangiji yace lokaci ya yi, magana ta kare.” “Yin abin da a wuri na ba daidai ba ne, ba zai kara mani kwana daya a gadon sarauta ba. Idan lokaci ya zo, zan bar kan karaga ko a raye, ko a mace.”

Ba za ayi ba daidai ba, in yi shiru “Watakila an yi gaskiya domin takardar da aka rubuto mani, ta zarge ni da ‘yi wa gwamnati rashin da’a.’” “Na zabi in hakura da sarauta domin in tsira da mutunci na, a maimakon in duka wa wani wanda giyar mulki ta dauke shi, da nufin in cigaba da sarauta.”

Labarai Makamanta

Leave a Reply