Dalilin Da Ya Sa Na Kauracewa Taron PDP – Jonathan

Rahotanni sun tabbatar da Tsohon shugaban ƙasa, Goodluck Jonathan, babban jigo a jam’iyyar PDP, bai sami halartar babban gangamin taron PDP na ƙasa ba wanda ya gudana ranar Asabar.

An ruwaito cewa Jonathan ya bar Najeriya ranar Asabar domin halartar taron ƙungiyar Nahiyar Africa a Nairobi, Kenya, wanda za’a tattauna kan zaman lafiya a Africa. Amma wasu ƙusoshin PDP na ganin tsohon shugaban ya yi amfani da wannan uzurin ne domin tsallake babban gangamin taron PDP.

Wani ƙusa a jam’iyyar PDP yace: “Idan har hankalinsa nakan taron, da kuma harkokin jam’iyya da ya halarci wurin na ɗan lokaci ya yi jawabi kafin ya tafi ranar Asabar. “Hakanan kuma zai iya turo tsohon mataimakinsa, Namadi Sambo, ko wani na kusa da shi, domin ya yi fatan alkairi a taron a madadinsa.”

Wata majiya daga cikin PDP, ta bayyana cewa gwamnan Bayelsa, Douye Diri, da takwaransa na jihar Oyo, Seyi Makinde, sun gana da Jonathan ranar Jumu’a. Majiyar ta ƙara da cewa lokacin da Jonathan ya faɗa musu zai tafi Nairobi, gwamnonin biyu sun bukaci ya halarci wurin taron na ƙanƙanin lokaci ya yi jawabi kafin ya tafi.

Hakanan gwamnonin sun masa tayin cewa zasu shirya masa tafiyar da zai yi bayan an kammala taron, amma tsohon shugaban ya ƙi amincewa.

Labarai Makamanta