Dalilin Da Ya Sa Na Kashe Ummu Kulthum – Dan Kasar Chaina

Labarin dake shigo mana daga jihar Kano na bayyana cewar Mutumin da ake zargi da kashe wata budurwa a Kano ɗan ƙasar Chaina Geng ya yi zargin cewa Ummu ta masa alƙawarin zata aure shi amma daga baya ta saɓa alƙawarin bayan ya kashe maƙudan kuɗi a kanta.

A jawabin da ya yi wa yan sanda, Ɗan China ya bayyana cewa saɓa alƙawarin ya fusata shi sosai, bisa haka zuciyarsa ta raya masa ya je har gida ya kasheta.

Mai magana da yawun rundunar ‘yan Sandan Jihar Kano Kiyawa ya ƙara da cewa Mahaifiyar yarinyar ce ta rinka kururuwar neman taimako lokacin da Geng ke aikata ɗanyen aikin kuma nan take aka sanar da yan sanda suka kai ɗauki.

Tuni dai kwamishinan yan sanda ya umarci DPO na Caji Ofis ɗin Ɗorayi Babba ya kula da lamarin, inji Kakakin yan sandan Kano.

Bayanai sun bayyana cewa a halin yanzun an maida ɗan Chinan sashin binciken mayan laifuka na Hedkwatar yan sanda dake Bampai, Kano domin tsananta bincike da kuma miƙa shi Kotu.

A ɗaya ɓangaren kuma, tuni aka Sallaci marigayya Ummu Kulthum aka kaita makwancinta ranar Asabar da Safe yayin da yan uwa da abokanan Arziki ke jimamin rasuwarta.

Labarai Makamanta