Dalilin Da Ya Sa Na Janye Daga Yin Sulhu Da ‘Yan Bindiga – Gumi

Mashahurin Malamin addinin Musuluncin nan mazaunin garin Kaduna Sheikh Dr. Ahmad Gumi, ya bayyana cewa ya daina sulhu da ‘yan bindiga ne saboda gwamnatin jihar ta nuna ba ta son haka.

Wannan ya biyo bayan harin da yan bindiga suka kai jami’ar Greenfield dake hanyar Abuja-Kaduna inda sukayi awon gaba da dalibai kuma suka kashe mutum daya.

A yayin da yake zantawa da manema labarai a ranar Alhamis, hadimin Gumi, Salisu Hassan, ya ce Malamin ya daina tafiya sulhu da ‘yan bindigan ne don bin umurnin gwamnatin jihar ta Kaduna.

“A’a, Sheikh ba wai yana da wasu ayyuka bane. Matsalar itace gwamnati ta ce bata son a yi sulhu da wadannan mutane,” Hassan yace. “Saboda haka Sheikh yana kokarin samar da wasu hanyoyin cimma manufarsa.

Idan baku manta ba, Dr Gumi ya shiga dazuka daban-daban a Arewa maso yammacin Najeriya don yiwa ‘yan bindiga wa’azin su ajiye makamansu, su yi sulhu da gwamnati, amma El-Rufa’i ya nuna baya son hakan.

Gwamnan Nasiru El Rufa’i ya ce zai hukunta duk wanda yayi sulhu da ‘yan bindiga da sunan gwamnati cikin gaggawa ba tare da ɓata lokaci ba.

Labarai Makamanta