Dalilin Da Ya Sa Ba Muyi Gwanjon Kayan Diezani Ba – EFCC

Rahotanni daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Shugaban hukumar hana almundahana da yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa watau EFCC, Abdulrasheed Bawa, ya bayyana cewa kayan adon da suka kwace daga hannun tsohon ministar mai, Diezani Alison-Madueke ya kai N14.4 billion.

Shugaban EFCC ya bayyana hakan ne ranar Juma’a yayinda ya gurfana gaban kwamitin majalisar wakilai dake bincike kan yadda akayi da kudaden satan da aka kwato, daga hannun barayin gwamnati.

Yace “kayan adon da aka kwata daga wajen tsohuwar ministar ya kai na kudi N14.4 billion, kamar yadda hukumomin gwamnati suka kiyasta.”

Bawa ya kara da cewa kiyasin kudin gidajen da aka kwace daga Diezani ya kai $80 million.

Amma har yanzu hukumar bata sayar da wadannan dukiyoyi ba saboda gwamnati bata bada umurnin haka ba, inji Bawa.

Majalisar wakilai ta fara kaddamar da bincike kan dukkan dukiyoyin da hukumomin gwamnati ta kwato tsakanin 2002 da 2020.

A watan Satumban 2019, babban kotun tarayya dake Legas ta sadaukarwa gwamnatin tarayya kayan adon Diezani Madueke. Diezani ta kasance Ministar Mai karkashin gwamnatin shugaba Goodluck Jonathan.

Labarai Makamanta