Dalilin Da Ya Sa Ba Mu Yi Hadaka Da Peter Obi Ba – Kwankwaso

Labarin dake shigo mana daga birnin Ikko na jihar Legas na bayyana cewar ɗan takarar shugabancin ƙasa ƙarƙashin inuwar Jam’iyyar NNPP Rabiu Musa Kwankwaso ya sake magana a kan dunkulewarsu da ‘yan jam’iyyar LP ta Peter Obi.

Sanata Rabiu Musa Kwankwaso yana cewa ba za ta yiwu jam’iyyar NNPP tayi tafiya da LP ba saboda sabani da aka samu. ‘Dan takaran shugaban kasar ya yarda cewa da sun yi taron dangi, zai fi sauki suyi nasara, yace wasu sun nuna dole a ba ‘Dan kudu maso gabas takara.

Kwankwaso ya yi wannan bayani ne a lokacin da aka bijiro masa da maganar yayin da ya tattauna da kungiyar ‘yan jarida na kasa kwanaki a birnin Ikko na jihar Legas.

Tsohon Gwamnan na jihar Kano yake cewa ya yi mamaki da ya ji wasu suna dauko wannan magana a halin yanzu bayan damar yin hakan ta shude masu.

“Mun wuce lokacin da za a hada wata alaka. Amma hakan abu ne mai kyau. Da an yi nasara, INEC ba za ta rika maganar kai zabe zagaye na biyu ba. Inda aka samu tababa shi ne a game da wanda za a ba takarar shugaban kasa da wanda za a tsaida ya zama ‘dan takarar mataimakin shugaban kasa.

A cewar Kwankwaso, an sa son kai a lamarin, ana ganin ba a taba samun shugaban kasa daga Kudu maso gabas ba, don haka dole ne sai an tsaida Peter Obi. Kwankwaso wanda yake harin mulki a zaben shekara mai zuwa yace a tsarin mulki, mutum ba zai iya zama shugaban kasa ba, sai ya samu kashi 25% a jihohi 25.

Labarai Makamanta