Dalilin Cire Salma A Shirin Kwana Casa’in – Daraktan Fim

Cikin wata tattaunawa da BBC Hausa tayi da Daraktan shirin fim ɗin Kwana Casa’in Salisu T. Balarabe, ya bayyana dalilinsu na sauya tauraruwar shirin Maryuda Yusuf wacce aka fi sani da Salma.

“Lokacin da muka shirya zamu fara ɗaukar shirin Kwana Casa’in Zango na shida mun tuntuɓi Salma, sai ta faɗa mana cewa gaskiya ba za ta samu dama ba.”

“Mun so mu san dalili sai ta faɗa mana cewa yana da nasaba da iyayenta wanda ba lallai ne ta iya bayyanawa ba.” Inji Darakta T. Balarabe

Labarai Makamanta