Dalilanmu Na Rufe Sansanonin ‘Yan Gudun Hijira – Zulum

Gwamna Babagana Zulum na Jihar Barno ya nuna farin cikin sa dangane da ci gaban da jihar sa ke samu wajen ƙarfafa tsaro. Sannan kuma ya yi addu’a Allah ya sa tsaron ya fi yanzu ƙaruwa a cikin 2022.

A saƙon murnar shiga sabuwar shekara da gwamnan ya fitar a ranar Asabar, Zulum ya ce gwamnatin sa za ta ci gaba ƙara yin hoɓɓasan ganin an kawo ƙarshen matsalar tsaro a Jihar Barno.

Daga nan kuma Zulum ya kare tare da bayar da hujjojin dalilan su na rufe sansanonin masu gudun hijira.

“Tilas su yarda cewa sai da rai ake samun abincin da za a rayu. Muna aiki ba dare ba rana domin ganin an wanzar da zaman lafiya wanda za mu iya bai wa jama’a garanti cewa za su iya fita neman abincin su cikin kwanciyar hankali.

“Cikin 2021 mun yi ƙoƙari tuƙuru wajen ƙara wa jami’an tsaron mu ƙarfi, har ma da ‘yan bijilante waɗanda muka bai wa kayan aiki da kuɗaɗen da za su yi ayyukan su sosai.

“Mun ga alfanun wannan ƙoƙarin cikin 2021, domin a shekarar ba a samu muggan hare-hare ba. Kuma sojojin mu sun yi rawar gani sosai.

“Duk da haka dai ba mu kai har inda muke son ganin mun kai wajen samar tsaro ba, amma dai mu na samun ci gaba sosai. Don haka ina mai tabbatar maku cewa na sadaukar da kai na wajen bayar da goyon baya ga dukkan ɓangarorin jami’an tsaron mu da jajirtattun ‘yan bijilante ɗin mu waɗanda ke taimaka mana.” Inji Zulum.

Da ya ke magana kan kwashe ‘yan gudun hijira ana maida su yankunan garuruwan su, tare da rufe sansanonin, Zulum ya ce ana yin haka ne domin a dawo wa mutane da martabar su sai kuma dalilai na daƙile ɓarnar da ya ce ta ke faruwa a cikin sansanonin.

Zulum ya lissafa baɗalar da ake yi a cikin sansanonin sun haɗa da karuwanci, sace-sace da shan muggan ƙwayoyi a cikin sansanonin masu gudun hijira.

Zulum ya ce gwamnatin sa na sake tsugunar da jama’a a bisa tsarin da duniya ta yarda da shi, kuma ake yi a duk duniya. Sannan kuma ya na tanadar masu da kayan tallafi idan sun koma mazaunan su.

“Gwamnatin mu ta fi fifita al’ummar Jihar Barno, domin mutanen mu su ne haƙƙin su ya rataya a wuyan mu.

“Mu na sane da cewa za su riƙa cin karo da ‘yan matsaloli ko ƙalubale yayin da su ka koma garuruwan su, ko inda aka sake tsugunar da su. Dalili kenan mu ke samar masu da tallafi iri daban-daban, domin ƙara masu ƙwarin guiwar zama a muhallan su.”

Zulum ya ce matsalar wutar lantarki a Maiduguri da kewaye na nan ana ƙoƙarin shawo kan aikin Tashar Samar da Gas a Maiduguri, wadda ya ce Gwamnatin Tarayya ta kusa kammala aikin nan ba da daɗewa ba.

Labarai Makamanta