Dalilanmu Na Hana Yin Sallah Da Lasifika – Saudiyya

Rahotanni daga birnin Riyadh na kasar Saudiyya na bayyana cewar Ƙasar Saudi Arabiya ta maida martani kan mutanen dake sukar matakin da ta ɗauka na rage ƙarar kiran sallah a masallatai.

Idan masu karatu za su tuna mun kawo muku rahoton cewa Saudiyya ta bada umarni ga masallatai su rage ƙarar lasifikokin su yayin kiran sallah.

Rahoton BBC ya nuna cewa ma’aikatar harkokin addinin musulunci ta ƙasar ta maida martani kan wasu mutane dake sukar matakin.

Abdul-lateef Sheikh ya bayyana cewa an ɗauki wannan matakin ne biyo bayan ƙorafe-ƙorafen da jama’a ke yi kan ƙarar kiran sallah.

Daga cikin waɗanda suka yi ƙorafin kan ƙarar ƙiran sallah, akwai iyaye waɗanda suka bayar da dalilin su cewa ƙarar lasifikun masallatai na hana ‘ya’yansu barci.

A makon da ya gabata ne, ma’aikatar ta umarci masallatai a ƙasar su rage ƙarar na’urar kiran sallah zuwa kashi ɗaya na ƙararta.

“Masu sukar wannan matakin maƙiya ne kuma masu son tada husuma a tsakanin jama’a.” Inji shi.

Labarai Makamanta