Dalilan Nada Yusuf Buhari Sarautar Talba – Masarautar Daura

Rahotanni daga masarautar Daura dake Jihar Katsina na bayyana cewar Mai martaba Sarkin Daura, Alhaji Umar Farouk, ya yi magana kan dalili da yasa aka nada Yusuf, dan Shugaba Muhammadu Buhari Sarautar Talba a Masarautar Daura.

Yusuf, wanda shine ɗa namiji tilo na Shugaba Muhammadu Buhari, a ranar Asabar, aka nada shi sarautar Talban Daura kuma Hakimin Kwasarawa.

Da ya ke jawabi a fadarsa yayin bikin nadin sarautar sabbin hakimai hudu, a ranar Alhamis, sarkin ya ce nadin zai hana Talban yawo zuwa Abuja da Yola, garin mahaifiyarsa, bayan wa’adin mulkin Buhari ya kare.

“Ko da baka kaunar Buhari, kan san cewa Daura a yanzu ta banbanta da yadda ta ke shekaru shida da suka gabata. Don haka, mun masa tukwici kan karamcin da ya yi mana, mun bawa dansa daya tak, Yusuf, sarautar Talban Daura. Hakan zai hana shi yawo zuwa Yola (garin mahaifiyarsa) da Abuja.

“Daga Jami’ar Fasahar Zirga-Zirga zuwa Kwallejin Fasaha ta Tarayya, ga tituna da wasu manyan ayyukan raya kasa da cigaba. A yau, Daura ta fi wasu jihohin Najeriya a bangaren cigaba.” Sarkin ya cigaba da cewa akwai ‘yan asalin Daura masu yawa da suka taka rawan a zo a gani, amma ba kowa ke son sarauta ba, amma dai Buhari ya ciri tuta a cikinsu.

Labarai Makamanta