Dalilan Da Ya Sa Muka Tura Karnuka Gadin Makarantu – Masari

Gwamnatin jihar Katsina ta ce karnukan za su dinga sanar da masu gadi da dalibai duk wani motsi ko bakuwar fuskar da ba su amince da ita ba ta hanyar haushi

Gwamntin jihar Katsina da ke arewacin Najeriya ta ce za ta tura karnuka domin aikin gadi a makarantun da ke fadin jihar.

Kwamishinan ilimi na jihar Dakta Badamasi Lawal Chiranci ya shaida wa BBC cewa jihar ta ware makudan kudade domin samar da tsaro a makarantun ciki har da kewaye su da kuma ajiye karnuka.

“Gwamnan jihar Katsina Alhaji Bello Masari ya ware zunzurutun kudi kimanin Naira miliyan 580 domin a gyara katangun makarantun da suka rushe, kuma a sanya waya a kewayen katangun, an kuma fitar da wata dabara ta samar da karnuka a kowacce makaranta.

Karnukan na iya shakar kamshin da ba su amince da shi ba, kuma da zarar karnukan sun yi haushi na wani abu da ba su amince da shi ba, masu gadi da dalibai da jami’an tsaro za su tabbatar da cewa akwai matsala a inda suka jiyo haushin wanda hakan zai taimaka matuka.”

Sai dai bai bayyana adadin karnukan da za a girke a makarantun ba da kuma kudin da za a kashe wajen dawainiyarsu.

Ya kara da cewa bisa al’ada karnukan da ake da su a gidaje kan yi haushi a duk lokacin da suka ga bakuwar fuska, ko motsin da ba su amince da shi ba. Domin haka gwamnati ta ba da shawarar a tanadi karnuka a makarantu, wadanda suke da su sai su kara inganta su.

“Wadannan karnuka za su yi tasiri saboda ba a Najeriya kadai ake amfani da dabba a matsayin tsaro, misali akwai inda suke amfani da kwakwa, ko jakuna saboda dalili na tsaro,” in ji Dakta Badamasi.

A cewarsa gwamnatinsu za ta fara bai wa dalibai ilimi kan tsaro, yana mai cewa “misali a lokacin da aka sace daliban makarantar kwana ta Kankara masu satar mutanen ne suka ce su dawo a lokacin da suka yi yunkurin tserewa, sai muke ganin da daliban na da ilimin tsaro da ba za a sace su da yawa kamar haka ba.”

Labarai Makamanta